Isra´ila ta ce ta yi amfani da makamin fosfa mai saurin kama wuta | Labarai | DW | 23.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta ce ta yi amfani da makamin fosfa mai saurin kama wuta

Isra´ila ta amsa cewa ta yi amfani da makamai masu dauke da hodar fosfa mai guba kuma mai saurin kama wuta a yakin da ta gwabza da ´yan Hisbollah a kudancin Libanon. Wani kakakin rundunar ´yan sandan kasar Yahudun Isra´ila ya tabbatar da haka bayan wani rahoto da jaridar Haaretz ta rubuta. Kakakin ya ce dokokin kasa da kasa sun yarda a yi amfani da irin wadannan makamai kuma sojin sa ba su aikata wani abin da ya sabawa doka ba. to sai dai kungiyar agaji ta Red Cross da kungiyoyin kare hakin bil Adama na matsa lamba da a gaggauta haramta amfani da wadannan makamai saboda mummunar kuna da suke janyowa.