1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta bai wa Yahudawa fifiko

Abdul-raheem Hassan
July 19, 2018

Majalisar dokokin Isra'ila ta amince da wata doka mai cike da takkadama kan amincewa da kasar a matsayin ta Yahudawa, tare da rage darajar yaren Larabci cikin manyan harsunan kasar.

https://p.dw.com/p/31jDb
Iran Parlament Tehran Mohammad Javad Zarif
Hoto: picture-alliance/EPA/A. Taherkenareh

Dokar ta samu amincewar 'yan majalisu 62 yayin 'yan majalisu 55 suka yi ki amincewa da kudurin, sai dai 'yan majalisu da ke wakiltar Larabawa a majalisar sun yi Allah wadai da matakin tare da nuna fargabar yunkurin murkushe 'yancin dimukuradiyya. Firaministan Isra'aila Benjamin Natanyahu ya jinjinya wa 'yan majalisar Isra'ila da suka yi fafatukar tabbatar da doka a mastayin yunkurin da ya shiga tarihin kasar.