1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta yarda da yarjejeniyar tsagaita wuta

May 21, 2021

Bayan kwashe tsawon kwanaki 11 suna luguden wuta a tsakaninsu, yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Faladinawa ta fara aiki tun da sanyin safiyar ranar Juma'a.

https://p.dw.com/p/3thfP
Palästina Feuerpause in Gaza
Hoto: Ibraheem Abu Mustafa/REUTERS

Rahotannin na cewa kasar Masar da ta shiga tsakani, zata tura da wakilai biyu zuwa Tel Aviv da kuma yankunan Falasdinawa don ganin yadda ake aiwatar da yarjejeniyar.

Tuni dai Faladinawa suka kaure da murna biyo bayan fara aikin tsagaita wutar, tare da daga tutoci da kuma harbi a iska a zirin Gaza. Bangarorin biyu dake rikici dai sun baiyana tsagaita wutar a matsayin nasara.