Isra′ila da Amirka na neman hanyoyin daidaita lamura | Labarai | DW | 09.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila da Amirka na neman hanyoyin daidaita lamura

Wannan ganawa ita ce ta farko tun bayan da kasashen yamma suka sa hannu kan yarjejeniyar kasa da kasa na makamashin nukiliyar Iran.

Shugaba Barack Obama na Amirka da Firaministan Israila Benjamin Netanyahu na neman hanyoyin samun daidaito a ganawarsu ta farko a fadar White-House tun bayan da aka sanya hannu kan yarjejeniyar kasa da kasa dangane da makamashin nukiliyar Iran, abin da ya janyo sa in sa tsakanin shugabanin biyu.

Kafin ganawar ta su dai, Netanyahu ya baiyana cewa Iran na janyo rashin daidaito a Yankin amma bai yi tsokaci dangane da makamashin nukiliyar ba.

Da yake jawabin maraba, shugaba Obama ya amince da cewa shi da takwaran na sa na Israila na da ra'ayoyi mabanbanta dangane da wannan batu amma kuma akwai wuraren da suka daidaita.

"Mun amince da juna idan ya zo ga batun cewa bamu su Iran ta mallaki makaman kare kisan dangi, ko kuma sa ido kan duk wani shirin da ka iya janyo matsala a yankin, saboda haka zamu tabbatar cewa mun sami amincewar juna a wadannan wurare."

Da yake mayar da martani, Netanyahu ya jaddada cewa a ya bayar da kai wajen wanzar da zaman lafiya, da samar da kasashe biyu wa al'ummomi biyu

"Bai kamata a yi shakkun cewa Israila a shirye take ta kare kanta daga barazanar ta'addanci ko rashin tsaro ba amma kuma duk da haka bai kamata a yi shakkar niyyar da take da shi na yin sulhun da duk makotanta da ke da niyyar yin sulhu"