Isira′ila ta kai sabbin hare hare a Gaza | Labarai | DW | 17.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isira'ila ta kai sabbin hare hare a Gaza

Dakarun Isira'ila sun yi kaca kaca da fadar gwamnatin Hamas a rana ta fuɗu ta faɗan da suke gwabzawa da mayaƙan ƙungiyar Hamas

Sojojin Isira'ila sun kai wasu sabbin hare hare na rokoki ta jiragen saman yaƙi a kan fadar gwamnatin Hamas da ke a yankin Zirin Gaza a ranar ta fuɗu a faɗan dake ƙara yin muni tsakanin sasan biyu.

Masu aiko da rahotanin sun ce jiragen yaƙi na Isira'ila sun yi wa cibiyar gwamnatin Hamas ɗin kaca kaca tare da lallata wasu gidajan jama'ar da ke kusa da fadar.Wani wanda ya ganewa idon sa abinda ya faru ya ce babu abinda ya yi sauran a ofishin.

A ƙalla falasɗiniyawa guda tallatin ne suka rasa rayukan su a ƙwanaki fuɗu na faɗa yayin da wasu 280 suka jikata.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu