Isaac Zida ya ƙaryata labarin yin murabus | Labarai | DW | 06.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isaac Zida ya ƙaryata labarin yin murabus

A ranar Lahadi ne wasu kafofin yaɗa labarai na kasar ta Burkina Faso suka ruwaito labarin shirin Firaministan na yin murabus daga kan muƙaminsa

A Burkina Faso Firaministan ƙasar Isaac Zida ya ƙaryata wata jita-jita da ke cewar ya yi murabus daga kan muƙaminsa:Ya bayyana hakan ne lokacin wani taron manema labarai da ya kira a wannan Litinin a cikin wata barikin sojojin birinin Ouagadougou jim kadan kafin ya tashi zuwa wata ziyarar aiki a kasar Cote d'Ivoire.Kusan mako ɗaya ke' nan dai da Firaministan rukwan ƙwaryar ƙasar ta Burkina Faso ke fuskantar barazana daga rundunar sojoji masu tsaron lafiyar shugaban ƙasa wato RSP wacce ta yi kira da ya yi murabus daga kan muƙaminsa.