IS ta kashe wani dan kasar Birtaniya | Labarai | DW | 14.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS ta kashe wani dan kasar Birtaniya

Birtaniya ta fara fuskantar fushin kungiyar IS, bisa abun da kungiyar ta kira marawa Amirka baya da Birtaniyan ke yi wajen murkusheta.

Kungiyar IS ta masu tsattsauran ra'ayin Sunna da ke gudanar da ayyukanta a Iraki da Siriya ta saki wani faifan Video da ke nuna yadda ta kashe wani jami'in bada agaji dan asalin kasar Birtaniya da ta ke tsare da shi. Kungiyar ta IS dai ta sace David Haines mai kimanin shekaru 44 a duniya a shekarar da ta gabata a yayin da ya ke gudanar da ayyukan agaji a Siriya. Haines dan asalin Scotland na aiki ne da wata kungiyar bada agaji ta kasar Faransa a Siriya yayin da 'yan IS din suka sace shi. Tuni dai Firaministan Birtaniya David Cameron ya yi Allah wadai da wannan aika-aika da kungiyar ta IS ta yi, tare kuma da shan alwashin kamo makasan Haines duk inda suke komai daren dadewa. Faifan Video dai ya yi kama da wanda kungiyar ta nuna yayin da ta hallaka 'yan jaridan nan biyu 'yan asalin Amirka a watan da ya gabata, kuma tace ta kashe Haines ne bisa irin rawar da Birtaniya ke takawa wajen ganin an kawo karshen ayyukanta.