IS ta kashe mayakan sa-kai a Iraki | Labarai | DW | 19.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS ta kashe mayakan sa-kai a Iraki

Kungiyar IS ta halaka wasu mayakan sa-kai 'yan Shi'a su 27 wadanda ke aiki da sojojin kasar Iraki, a yankin kudu maso yammacin birnin Kirkuk.

Mayakan kungiyar IS a kasar Iraki, sun halaka wasu mayakan sa-kai 'yan Shi'a su 27 wadanda ke aiki da sojojin kasar, a yankin kudu maso yammacin birnin Kirkuk. Lamarin dai ya faru ne yayin da mayakan na IS suka yi wa 'yan Shi'an kwantan bauna lokacin wani sintirin dare, kamar yadda majiyar mayakan na sa kai ta tabbatar.

Maharan na IS sun yi badda sawu ne cikin kayan soji, inda suka afka masu, suka kuma yi musayar wuta na akalla sa'o'i biyu. Wasu bayanai ma dai sun tabbatar da mutuwar wasu daga cikin mayakan na tarzoma.