1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta kashe farar hula 30 a birnin Al-Bab

Gazali Abdou Tasawa
December 26, 2016

Mahukuntan sojan kasar Turkiyya sun zargi Kungiyar IS da halaka wasu fararen hula 30 wadanda suka yi kokarin tserewa daga birnin al-Bab wanda ke zama wata tungar Kungiyar IS a Arewacin Siriya. 

https://p.dw.com/p/2UsyK
Syrien al-Bab Angriff auf IS-Stellung
Hoto: Getty Images/AFP/S. Ghaloun

 

Rundunar sojin kasar ta Turkiyya ta ce mayakan Kungiyar ta IS sun halaka mutanen ne a jiya Lahadi a lokacin wani hari da suka kai masu. Makonni da dama kenan da da sojojin kasar ta Turkiyya da hadin gwiwar 'yan tawayen Siriya suka kaddamar da farmaki kan birnin na al-Bab wanda suke neman kwacewa daga hannun Kungiyar ta IS da har yanzu ke ci gaba da yin turjiya. 

Ko a ranar Larabar da ta gabata  dai mayakan Kungiyar ta IS sun halaka sojojin Turkiyya 16 wanda ya zama barna mafi girm da mayakan Kungiyar ta IS suka taba yi wa sojojin Ankarar tun bayan soma fadan a watan Agustan da ya gabata.