IS ta dauki alhakin sabon harin Kabul | Labarai | DW | 29.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS ta dauki alhakin sabon harin Kabul

Rahotanni daga Afganistan na cewar wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a babbar cibiyar horan sojoji ta kasar da ke a birnin Kabul.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa an kai harin ne da misalin karfe biyar na safiyar wannan Litinin da rokoki da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma gurneti-gurneti inda aka share sama da awoyi uku ana ba ta kashi tsakanin maharan da jami'an 'yan sanda. Wata majiyar tsaro ta gwamnatin kasar ta Afganistan ta tabbatar da mutuwar hudu daga cikin maharan wadanda yanzu haka sojojin rindunar musamman na gwamnatin ta Afganistan suka yi nasarar yi masu kofar raggo. 

Uku daga cikin 'yan sandan kasar ta Afganistan sun jikkata a cikin harin na cibiyar horan sojojin ta Academi Marshall Fahim ta birnin Kabul da ke zama cibiyar horan sojoji mafi girma a kasar. Wannan shi ne hari na uku da birnin na Kabul ya fuskanta a cikin kwanaki goma na baya bayan. Tuni kuma Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wannan hari.