Iran: Zanga-zangar neman sakin Zakzaky | Labarai | DW | 18.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran: Zanga-zangar neman sakin Zakzaky

Masu fafutikar kare hakkin bil Adama dai na cewa mutanen da suka rasu sakamakon rikicin sun kai mutum dubu daya.

Iran Protest

Al'ummar Iran na zanga-zanga

Dubban al'ummar kasar Iran mabiya tafarkin Shi'a sun gudanar da zanga-zanga a titunan birnin Teharan a wani bangaren na nuna takaicinsu a kisan da aka yi wa daruruwan 'yan uwansu a wannan tafarki da ke a Najeriya.

Daruruwan 'yan Shi'a ne dai ake sa ran sun halaka bayan wata taho mu gama da jami'an tsaro a ranar Asabar da ta gabata a Najeriya. Shi dai shugaban mabiya wannan tafarki na Shi'a malam Ibrahim el-Zakzaky ya samu raunika sakamakon harbin bindiga a lokacin wannan taho mu gama da jami'an soji na kasar.

Masu fafutikar kare hakkin bil Adama dai na cewa mutanen da suka rasu sakamakon rikicin sun kai mutum dubu daya. Su dai masu zanga-zangar na birnin Tehran sun bukaci sakin malam Zakzaky ba tare da gindaya wasu sharuda ba.