1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar nukilyar Iran

Binta Aliyu Zurmi
September 7, 2019

Kasar Iran ta bayyana cewa za ta kara yawan makamashin nukilyar da take amfani da shi wajen sarrafa makamashi, fiye da wanda yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da kasashen duniya a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/3PDuE
Iran Atomprogramm
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Forutan

Hakan dai na nuna yadda Iran din ta dauki mataki na uku na janyewa daga yarjejeniyar da suka cimma, a daidai lokaci da take gargadi ga kasashen Turai kan cewa wa'adin da ta debar musu na su samarwa Tehran din mafita kan halin matsin tattalin arzikin da takunkuman Amirka da ta mayar mata ya jefa ta, tana mai cewa lokacinsu kurarre ne.

A wani labarin kuma, Iran din ta sanar da kara kame wani jirgin ruwan dakon mai tare da tsare matuka da ma'aikatan jirgin da suka kasance 'yan kasar Philipphines, yayin da rahotanni kuma ke nunar da cewa an hangi tankar dakon man Iran din a kan hanyarta ta zuwa gabar Tekun Siriya. A kwanakin baya dai Birtaniya tsare tankar bisa zargin Iran din na son safarar man zuwa Siriya ba bisa ka'ida ba, sai dai Iran din ta musanta hakan.