Iran ta yi watsi da zargin Saudiyya | Labarai | DW | 31.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi watsi da zargin Saudiyya

Gwamnatin Iran ta ce kasashen yankin Gabas ta Tsakiya na mata zargi mara tushe kan ta'addanci a taron koli na gaggawa da kasashen ke yi a Makka.

Saudiyya na neman hadin kan kasashen Amirka da Isra'ila da sauran kasashen duniya domin dakatar da Iran daga yunkurin yi wa yankin Gabas ta tsakiya barazana.

Sarki Salman bin Abdul'azeez al-Sa'ud ya Iran da tallafawa ta'addanci tare da neman kaiwa jiragen dakon man ta harin, amma kasar Iran ta musanta wannan zargi tare da cewa yunkuri ne kawai na neman yi mata taron dangi. A baya-bayannan dai Amirka na cigaba da jibge tannkokin yaki da sojoji a yankin Gabas ta tsakiya a wani mataki na yi wa Iran barazana daukar wani mataki da zai kai ga tada yaki.