1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tehran ta sallami Faransawa daga kasar

Ramatu Garba Baba
May 12, 2023

Faransawa biyu gwamnatin Tehran ta sallama daga gidan yarin kasar bayan sun shafe lokaci suna zaman kurkuku kan zarge-zargen take wasu dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/4RI2j
Turawan da Iran ta yi wa afuwa
Turawan da Iran ta yi wa afuwaHoto: Family Handout/S. Dehghan's Twitter account/AFP

Wasu Turawa biyu na kan hanyarsu ta komawa Faransa, bayan da aka sako su daga wani gidan yarin Iran a wannan Jumma'ar. Bafaranshe Benjamin Briere mai shekaru 37 da haihuwa, ya dai kwashi shekaru uku a gidan yari kan laifin daukar hotuna a wasu wuraren da gwamnatin Tehran ta haramta a yayin da aka yanke wa dan kasar Ireland mai jini da Faransa Bernard Phelan hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa laifin leken asiri, dan shekaru 64 da haihuwar, ya yi zaman gidan yarin na watanni bakwai kafin a cimma matsaya a tsakanin Iran da Faransa.

Jim kadan da bayar da umarnin su bar kasar, Shugaba Emmanuel Macron na Faransan ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter, ya na mai baiyana jin dadinsa tare da cewa, sabon babi kasashen biyu suka bude na fatan gina dangantakar aminta da juna.