1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Amirka da Iran a New York

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 11, 2019

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bukaci Amirka da ta sallami duk wasu masu neman jefa ta cikin yaki daga gwamnati.

https://p.dw.com/p/3PQI1
Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Shugaban Amirka Donald Trump da Hassan Rouhani na IranHoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Kalaman na Rouhani dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar fargabar barkewar rikici a yankin Gabar Tekun Fasha, sakamkon karuwar takun saka tsakanin Washington da Tehran, da kuma fargabar karasa rugujewar yarjejeniyar nukilyar da kasashen duniya masu fada aji suka cimma da Iran din.

An kuma bayyana kalaman na Rouhani a matsayin wani mataki na yabawa korar da Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi wa mai ba shi shawara kan harkar tsaro John Bolton daga bakin aiki, mutumin daministan harkokin kasashen ketare na Iran din Mohammad Javad Zarif ya bayyana da mai son a afkawa Iran da yaki.

Bolton dai ya jima yana sukar Tehran, inda ma ya taba cewa za su yi bikin rusa gwamnatin Iran. Akwai dai rade-radin cewa Trump ya kori Bolton ne, a wani yunkuri na son ganawa da shugaban Iran Hassan Rouhani yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, da za a yi cikin wannan wata na Satumba a birnin New York na Amirkan. Babu dai tabbacin ganawar za ta yiwu, sai dai kalaman Iran din na nuni da cewa Tehran ta ma fi jin haushin Bolton fiye da Trump.