1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta rataye tsohon mataimakin ministan tsaron kasar

January 14, 2023

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya nuna takaicinsa a kan wannan kisa. Ita dai Iran ta ce Akbari ya bayar da bayanan sirrin da suka kai ga kashe mata wani kwararran masanin makamashin nukiliya a shekara ta 2020.

https://p.dw.com/p/4MBty
Hoto: saednews

Iran ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga tsohon mataimakin ministan tsaron kasar da ke da takardar shaidar zama dan kasar Birtaniya Ali Reza Akbari.

Hukumomin Tehran sun rataye tsohon jami'in ne bisa laifin kwarmata wa hukumar leken asirin Burtaniya sirrikan kasar da suka ce ya aikata. Kafin kisan da Iran ta yi masa sai da ta sanya wani bidiyo na shi inda aka umurce shi da ya amince cewa ya aikata laifin da aka zarge shi da aikatawa.