Iran ta jaddada ′yancinta na shirin nukiliya | Labarai | DW | 07.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta jaddada 'yancinta na shirin nukiliya

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya ce ƙasarsa na da 'yancin gudanar da shirinta na nukiliya a cikin ƙasar.

Mr. Zarif ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi a birnin Tehran da takwaransa na Switzerland Yves Rossier, inda ya sake jaddada cewar Iran na da dukkannin 'yanci na gudanar da shirin na makamshin nukiliya na zaman lafiya ba tare da an yi mata katsalandan ba.

Isra'ila da ƙasashen yammacin duniya dai na zargi Iran ɗin da amfani da shirin wajen ƙera makaman ƙare dangi sai dai Iran din ta nace shirin nata na zaman lafiya ne, hasalima ta ce shiri ne na samar da makashi. A tsakiyar makon gobe ne dai ake sa ran komawa kan taburin tattaunawa kan shirin na nukiliyar Iran tsakaninta da ƙasashen da suka hada da Birtaniya da Faransa da China da Rasha da Amirka da kuma Jamus.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane