Iran ta cika sharuddan IAEA | Labarai | DW | 20.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta cika sharuddan IAEA

Iran ta amince ta lalata wani tarin nukiliyar da ta inganta wanda ake gani shi ne mafi hatsari, domin mututnta yarjejeniyar da ta kulla da kasashen yamma wanda zai rage mata takunkumi

Iran ta amince ta lalata ajiyanta na wani nau'in iskar Urainium din da ta inganta, a karkashin wata kwarya-kwaryar yarjejeniyar da ta kulla da kasashe shidda masu karfin tattalin arziki a bara, wadanda suka hada da kasashe biyar masu kujerun dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da Jamus.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ne ya samo wannan labarin daga rahoton da hukumar sanya ido kan makamashi nukiliyar Majalisar Dinkin Duniya wato IAEA kan fitar wata-wata.

Wannan rahoton na IAEA ya nuna cewa Iran ta cika duka sharuddan da yarjejeniyar na watanni shidda ta gindaya wanda da ma ake sa ran wa'adin ta zai kare a ranar 20 ga watan Yuli, amma kuma aka amince a kara, tare da kwaskware wasu abubuwa, bayan da suka gaza cimma yarjejeniyar karshe wanda zai kawo karshen kace-nace kan makashin nukiliyar tsakanin Iran din da takwarorinta na Yamma.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman