Iran ta ce ′yan kasarta ne maharan birnin Tehran | Labarai | DW | 08.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta ce 'yan kasarta ne maharan birnin Tehran

Kasar Iran ta ce maharan da suka afka wa babban birnin kasar a ranar Laraba, wasu 'yan kasar ta ne da ke cikin kungiyar IS a kasashen Iraki da kuma Syria.

Mahukuntan kasar Iran sun ce maharan da suka afka wa kasar a wannan Laraba, wasu 'yan kasar ne da ke cikin kungiyar IS da ke gwagwarmaya a kasashen Iraki da kuma Syria. Ma'aikatar leken asirin kasar ta ce biyar daga cikin maharan wadanda aka kashe su lokacin da suka kai harin, mutane ne da suka hakkake su a matsayin mayakan jihadi na IS.

Rundunar mayakan kundumbalan kasar ta zargi kasar Saudiyya da hannu cikin lamarin, a kokari na ta'azzara lamura tsakanin Sunni da kuma bangaren Shi'a da ke Iran din. A ranar Laraba dai kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a majalisar dokokin Iran da kuma hubbaren Ayatollah Khomeini inda mutane 17 suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata.