Iran ta ce ta shiga sahun ƙasashe masu fasahar nulikiya | Labarai | DW | 12.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta ce ta shiga sahun ƙasashe masu fasahar nulikiya

Shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad, ya tabbatar da cewa ƙasar sa, ta sami nasarar aiwatar da sarrafa sinadarin Uranium ɗin da ta ke buƙata domin samar da makamashin nukiliya. A jawabin da ya yiwa alúmar ƙasar a garin Mashhad, Ahmedinejad, yace a yanzu Iran ta shiga sahun ƙasashe masu fasahar nukiliya a duniya. Ya ƙara da cewa babbar manufa a yanzu, ita ce ta cigaba da gagarumin aikin sarrafa sinadarin na Uranium mai yawa. Ana iya yin amfani da makamashin na Uranium wajen ƙera makamin Atom, sai dai kuma Ahmedinejad ya nanata cewa ƙasar sa, ba ta da wani mugun nufi. Sanarwar ta zo ne makwanni biyu kafin ƙarewar waádin da majalisar ɗinkin duniya ta baiwa ƙasar Iran, ta dakatar da shirin nukiliyar ko kuma ta fuskanci hukunci mai tsanani. Shugaban hukumar majalisar dinkin duniya mai lura da hana yaduwar makaman nukiliya Mohammed el-Baradei zai kai ziyara kasar ta Iran. A waje guda kuma, Amurka ta mayar da martani da cewa Iran ta kaucewa hanya a kudirin ta na mallakar makamashin nukiliya.