1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce Isra'ila ce ta kashe Fakhrizadeh

Ahmed Salisu
November 28, 2020

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce Isra'ila da Amirka ne ke da hannu wajen kisan fitaccen masanin makamshin nukiliyar nan na kasar Mohsen Fakhrizadeh wanda ya rasa ransa sakamakon harbe shi da aka yi.

https://p.dw.com/p/3lxGN
Mohsen Fakhrizadeh |  iranischer Atomwissenschaftler
Hoto: IRNA

A wata sanarwa da Shugaba Rouhani din ya fidda ta kafar talabijin din kasar, ya ce Isra'ila da Amirka na da hannu dumu-dumu a kisan da aka yi wa mutumin mai suna Mohsen Fakhrizadeh dan shekaru 63 da haihuwa.

To sai dai duk da kisan na Fakhrizadeh, Iran din ta ce ba za ta yi sanyi gwiwa ba wajen cigaba da abin da ta sanya a gaba kamar yadda shugaban hukumar kula da makamashin nukliya na kasar Ali Akber Salehi ya bayanna.

Tuni dai Isra'ila ta tsaurara matakan tsaro a kan ofisoshin jakadancinta da ke kasashen duniya don gudun abin da ka je ya komo yayin da Jamus da sauran kasashe ke kiran da a kai zuciya nesa.