1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutum uku

May 19, 2023

Gwamnatin kasar Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutum uku da ta zarga da kasancewa cikin wadanda suka gudanar da mummunar zanga-zangar adawa da ita a bara.

https://p.dw.com/p/4RYu8
Hoto: Allison Bailey/NurPhoto/picture alliance

Shafin Intanet na kotun Mizan da ke Iran din, ya sanar da aiwatar da hukuncin kisan ne a kan Majid Kazemi da Saleh Mirhashemi da kuma Saeed Yaghoubi da jijjifin safiyar wannan Juma'ar.

Hukumomin na Iran dai sun ce mutanen uku sun kashe wasu jami'an 'yan sanda biyu a cikin watan Nuwamba lokacin gangamin nuna kyama ga gwamnatin a shekarar da ta gabata.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama wadanda da ma suka yi ta yi tir da wannan hukuncin, sun ce an azabtar da mutanen uku da aka kashe a yau tare da tilasta musu amsa laifi a kafofin talabijin, sannan kuma ba a bi shari'ar yadda ya kamata ba.