1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa tsakanin Iran da Taliban

Zulaiha Abubakar
December 26, 2018

Kasar Iran na gudanar da wata tattaunawa tare da kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan kamar yadda babban jami'in hukumar tsaron kasar ta Iran ya shaidawa manema labarai a wannan Larabar.

https://p.dw.com/p/3AeWk
Iran Rohani Hauhaltsrede im Parlament
Hoto: Getty Images/AFP/A. Kenare

Tattaunawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan samun rahoton wani zama tsakanin kungiyar ta Taliban da kasar Amirka kan matakan tsagaita wuta a kasar Afghanistan gabanin janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen ketare daga kasar. A farkon wannan wata ne dai jami'an tsaron Afghanistan din suka sanar da janyewa daga yammacin kasar da ke da iyaka da Iran, biyo bayan jinkirta wadata jami'an tsaron da wadatattun kayan aiki daga bangaren gwamnati. Ana sa ran wannan tattaunawar za ta kawo karshen yawan hare-hare a kasar ta Afghanistan.