1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin dakon kaya ya hallaka mutum 15

Ramatu Garba Baba
January 14, 2019

Mutum goma 15 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hadarin jirgin sama mai dakon kaya da ya yi yunkurin kaucewa hadari ta hanyar saukar gaggawa a Tehran.

https://p.dw.com/p/3BWGJ
Flash-Galerie Iran bildergalerie 02-11
Hoto: Ipa

Jirgin kirar Boeing 707 ya fuskanci matsala bayan tashinsa, lamarin da ya tilasta masa neman yin saukar gaggawa. Rahotannin daga kasar  Iran sun nunar cewa, jirgin ya kaucewa hanya a yayin da ya ke kokarin saukar, kafin daga bisani ya kama da wuta. Akwai wani mutum guda da aka ce ya yi nasarar tsira da ransa.