Iran: Iraki ba za ta taimaki Amirka ba | BATUTUWA | DW | 17.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Iran: Iraki ba za ta taimaki Amirka ba

Jakadan kasar Iraki a kasar Rasha ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa, ba za ta amincewa Amirka ta yi amfani da kasar domin kai wa kasar Iran hare-hare ba.

Das Flugdeckpersonal steht an Bord des Flugzeugträgers USS Abraham Lincoln der Nimitz-Klasse (Reuters/J. El Heloueh)

Mirka ta jibge kayan yaki a yankin Tekun Farisa

Adaidai lokacin da Amirka ke karfafa damararta a yankin Gabas ta Tsakiya biyo bayan takun sakar da ta barke tsakaninta da Iran, kasar Iraki da ke zama daya daga cikin manyan sansanonin Amirka a yankin, ta ce ba za ta lamunta Amirkan tayi amfani da sansanoninta da ke cikin kasarta don kai wa Iran hari ba. Ga dukkan alamu dai matsin lambar da Amirkan ke yi wa mahukuntan Irakin kan su yaye wa kasar Iran baya, ya gaza cimma nasara, inda Irakin ba ta tsaya ga zama 'yan ba ruwanmu ba, har ma ta fito karara ta nuna cewa ba za ta goyi bayan ayi amfani da ita a cutar da makwabciyarta Iran ba. Tashar talabijin ta Press TV a Tehran fadar gwamnatin Iran din, ta nakalto jakadan kasar Irakin a Mosco Haidar Mansour Hadi Al-Athari yana mai bayana matsayar kasar tasa a ranar Laraba. Mansour Hadi Al-Athari ya kara da cewa kasar Iraki ba ta son wani sabon rikici a yankin tekun Farisa, yana mai cewa kasarsa kasa ce mai cikakken 'yancin kanta. Ya ce Iraki ta zabi ta zama mai shiga tsakani a rikici tsakanin Tehran da Washington da ke neman kara kamari a cikin 'yan kwanakin nan.

Irak Adel Abdul Mahdi (Getty Images/AFP/Y. Al-Zayyat)

Firaministan kasar Iraki Adil Abdul-Mahdi

Kafin haka dai Firaministan kasar ta Iraki Adil Abdul-Mahdi ya tabbatar da cewa idan har yaki ya barke tsakanin Tehran da Washington, to kuwa gwamnatin Iraki ba zata bar Amirka ta yi amfani da kasar don kai wa kasar Iran hare-hare ba. To sai dai a ta bakin Hashim Muntasir wani dan jam'iyyar adawa na Irakin, kalaman mahukuntan Iraki na hana Amirka amafani da kasar don kai wa Iran hari ihu ne ka wai bayan hari yana mai cewa gwamnatin 'yar amshin shatar kasashen Amirka da Iran ce. Ya kara da cewa dukka kasashen biyu ka iya yin amfani da Iraki domin cimma muradunsu a karkashin wannan gwamnatin. Hakan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da shugaban majalisar dokokin Kuwait Marzuq Ganeem ke kashedin barkewar yaki nan kusa a yankin. A makon da ya gabata ne sakataren harkokin wajen kasar Amirka Mike Pompeo ya ce kasarsa ta sami rahotannin sirri na cewa Iran barazana ce ga tsaron Amirka a yankin Tekun Farisa, baya ga haka akwai wasu kawayen Amirkan a yankin wadanda Iran ke zama barazana a garesu. Da wannan dalilin ne Washington ta aike da karin sojojinta a yankin Tekun Farisa daga ciki har da jirgin ruwan nan mai daukar jiragen yaki wanda ake kira Ibraham Abraham Lincoln. 

Sauti da bidiyo akan labarin