Iran: An harbo jirgi maras matuki | Labarai | DW | 08.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran: An harbo jirgi maras matuki

Hukumar tsaro a kasar Iran ta sanar da harbo wani jirgin sama maras matuki a Kudu maso Yammacin kasar

Tuni gwamnan yankin da wannan al'amari ya faru Gholamreza Shariati yayi wa manema labarai karin haske da cewar, jirgi ne mallakar kasashen ketare wanda jami'an tsaro ke aikin binciken baraguzan jirgin don gano bayanan da ke kunshe cikinsa.

Sanarwar ta kara da cewar shawagin jirgin maras matuki a yankunan kasar ta Iran karya dokar amfani da sararin saman kasar ne wanda kundin tsarin mulkin kasa yayi tanadi, wannan al'amari na zuwa ne yayin da Iran ta yi watsi da yarjejeniyar sarrafa makamashin nukiliya sakamakon janyewar Amirka daga yarjejeniyar a shekarar data gabata.