Iran: An cafke masu hannu a harin juma′a da ta gabata | Labarai | DW | 10.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran: An cafke masu hannu a harin juma'a da ta gabata

Hukumomin kasar Iran, sun tabbatar da kame mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen kai harin bam a majalisar dokokin da ke Tehran.

Tun da farko ranar Jum'a da ta gabata humomin tsaro sun kame mutane 41 da ake tunanin suna da hannu a tagwayen hare-haren da suka yi  sanadiyyar mutuwar mutane 17 a majalisar dokokin kasar. Jami'an 'yan sanda na Iran din, sun kuma gano motar da maharan suka yi amfani da ita wajen kai hare-haren biyu na ranar Laraba a tsakiyar birnin kasar. Tuni dai Kungiyar IS ta dau alhakin kai wannan mummunan harin.