1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta haramta dangantaka da Isra'ila

Abdul-raheem Hassan
May 27, 2022

'Yan majalisar dokokin Iraki sun gabatar da kudirin doka da zai haramta yin ko wace irin alaka ko dangantakar kasuwanci da kasar Isra'ila, dokar ta bukaci hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai.

https://p.dw.com/p/4BvGW
Irak Bagdad | Parlamentssitzung Januar 2022
Hoto: Iraqi Parliament Press Office/Handout/AA/picture alliance

Dokar ta samu amincewar 'yan majalisu 275 cikin 329, inda suka kare matsayarsu da cewa shi ne zahirin abin da 'yan kasar Iraki ke bukata. Sai dai tuni gwamnatin Amirka ta yi tir da wannan doka, tare da yin gargadin cewa dokar barazana ce ga ci gaban kasar da kuma takaita 'yancin dan Adam da haddasa fargaba ga kasashe makwabta.

Dama dai Iraki ba ta amince da Isra'ila ba tun kafuwar kasar a shekarar 1948, wannan ya sa kasashen biyu ba su da dangantakar diflomasiyya.

A farkon shekarar 2022, Iran ta harba makami mai linzami guda 12 zuwa birnin Irbil da ke arewacin kasar Kurdawa da zimmar kai farmaki kan sansanin leken asirin Isra'ila.

Rahoton kwamitin bincike na majalisar dokokin Iraki ya ce ba a sami wata hujja da za ta goyi bayan zargin da Iran ta ke yi na cewa akwai sansanin leken asirin Isra'ila a Irbil ba.