Iraki ta fara samun jiragen yaki daga Rasha | Labarai | DW | 29.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki ta fara samun jiragen yaki daga Rasha

Dakarun Iraki na ci gaba da fafatawa da tsagerun masu dauke da makamai, domin sake kwato wasu sassan kasar

Dakarun kasar Iraki da ke samun tallafin jiragen saman yaki, suna ci gaba da zurfafa hare-haren da suke kai wa cikin yankunan arewa da tsakiyar kasar da ke hannun tsagerun masu kaifin kishin Islama na kungiyar ISIS. Tun farko sun bayyana nasarar kwace garin Tikrit, mahaifar tsohon Shugaban kasar Marigayi Saddam Hussein. Wani babban jami'in gwamnatin kasar ya ce, suna suna tsara dabara tare da mahukuntan Amirka kan yadda za a kawar da tsagerun.

Kasar ta Iraki ta bayyana karbar biyar daga cikin jiaragen saman yaki 25 da ta saya daga hannun kasar Rasha bisa wata yarjejeniya da suka kulla. Shugabannin jam'iyya mai mulki suna tattaunawa kan maye gurbin Firaminista Nouri al-Maliki, domin kafa gwamnatin da za ta kunshi duk bangarorin kasar ta Iraki. Masu kula da abubuwan da ke wakana a kasar sun nunar da cewa karfi kawai ba zai iya shawo kan rikicin kasar ba, sai an hada da sasantawa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar