Iraki ta ce Saudi da Qatar ne ke rura wutar rikicin kasar | Labarai | DW | 09.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki ta ce Saudi da Qatar ne ke rura wutar rikicin kasar

Firaministan Iraki Nuri al-Maliki ya ce mahukuntan Saudiyya da Qatar ne ke tallafawa 'yan bindigar kasar wadan ke cigaba da tada zaune tsaye a sassa daban-daban na Iraki.

Al-Maliki ya ambata hakan ne a wata hira da aka yi da shi a jiya, daidai lokacin da Irakin ke cigaba da fuskantar hare-haren kunar bakin wake wanda kasar ba ta ga irinsa ba tun cikin skerara ta 2008.

Firaministan na Iraqi ya ce yanzu haka wadannan kasashe biyu na taimakawa 'yan tawayen kasar da kudade da kuma tallafi ta bangaren watsa labarai, lamarin da ya ce daidai ne da tallafawa aiyyukan ta'addanci a duniya.

Dama a cikin watan Janairun da ya gabata al-Maliki ya ambata cewar awkai wasu kasashen da ke dafawa 'yan bindigar kasarsa sai dai bai kai ga bayyana sunayen ba sai a jiya Asabar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh