1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki na nema ta zamo makabarta

October 20, 2013

A kullum sai kara kai hare-haren kunar bakin wake a ke a kasar Iraki wanda hakan ke sanya fargabar sake fuskantar yakin banbancin akida a kasar.

https://p.dw.com/p/1A2pq
Hoto: Reuters

Wasu 'yan kunar bakin wake takwas sun kai hare-hare a ofisoshin 'yan sanda da na gwamnati a birnin Rawa, dake arewa maso yammacin Bagadaza babban birnin kasar Iraki, inda suka hallaka mutane takwas yayin da wasu bakwai suka rasa nasu rayukan a wasu hare-haren kunar bakin waken na daban da aka kai a wasu sassan kasar.

Wadannan hare-hare dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ke fuskanta yanayi mafi muni na tashe-tashen hankula tun bayan zubar da jinin da aka yi a shekara ta 2008, yayin rikicin babancin akida da kasar ta sha fama da shi, inda kuma a hannu guda ake fargabar yakin da ake gwabzawa a Siriya dake makwabtaka da Iraki ka iya shafar ta.

Harin na yau dai yayi sanadiyyar mutuwar kananan jami'an 'yansandan yankin na Rawa dake gundumar Anbar uku da kuma wasu 'yan sanda uku da dan karamin yaro da kuma wani farar hula.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar.