1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu jinyar corona sun mutu a gobara

Binta Aliyu Zurmi
April 25, 2021

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyar gobarar da ta tashi a asibitin Ibn-Khatib da ke gabashin Bagadaza ya haura mutum 80.

https://p.dw.com/p/3sYSe
Irak | Corona-Intensivstation | Mehr als 20 Tote bei Brand in Krankenhaus in Bagdad
Hoto: Murtadha Al-Sudani/AA/picture alliance

Da dama daga cikin wadanda gobarar ta rutsa da su na masu dauke da cutar corona ne da suke kan na'urar da ke taimakawa marasa lafiya numfashi. An dai alakanta tashin gobara daga yoyon  tukwanan iskar gas.

Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce ko baya ga wadanda suka kone kurmus a gobarar wasu sun mutu a sakamakon hayakin da suka shaka yayin da wasu kuma suka mutu sanadin cire su da aka yi daga na'urar ventilator da ke taimakawa mutum wajen yin numfashi.

Tuni dai Firaminista Mustafa al-Kadhemi ya sanar da dakatar da ministan lafiyar kasar bayan wannan mumunar gobara, lamarin da ke ci gaba da jan hankulan al'umma da ke bukatar korar ministan daga aiki maimakon dakatar da shi na wani lokaci.