Iraki: Dubban kananan yara na cikin hadari a Mossul | Labarai | DW | 05.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki: Dubban kananan yara na cikin hadari a Mossul

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce akalla yara dubu 100 ne ke cikin hadari a birnin Mossul, inda sojojin gwamnati ke kokarin kwato yankin da ya rage a hannun mayakan IS.

Irak Region Mossul Hammam al-Alil Flüchtlinge (Reuters/T. Al-Sudani)

Yana da iyayensu yayin da suke tserewa rigingimu daga birnin Mossul

Asusun na UNICEF ya ce yaran da suka hada da maza da mata na cikin babban hadari ne a tsohon birnin Mossul, da kuma sauran wasu yankuna na yammacin birnin, inda suke tsakanin huta biyu ta mayakan IS da kuma dakarun gwamnatin Iraki, sannan hare-haren da ake kaiwa sun shafi har da manyan asibitoci da kuma wasu wuraren kiwon lafiya a cewar UNICEF.

Asusun kula da kananan yaran na UNICEF ya yi kira ga bangarorin biyu da su mutunta dokokin kasa da kasa ta hanyar bada kariya ga wadan an yara da ke neman hanyoyin ficewa daga inda suke. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, fiye da mutane dubu 750 ne suka bar gidajensu tun daga farkon wannan samame na neman kwato birnin na Mossul a watan Oktoban bara.