1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki bayan shekaru hudu

April 10, 2007

Yau talata ne aka samu shekaru hudu da kifar da mulkin Saddam hussein, amma Iraki bata samu zaman lafiya ba

https://p.dw.com/p/Btvq
Sojan Amurka a Iraki
Sojan Amurka a IrakiHoto: AP

Ko da yake a ranar tara ga watan afrilun shekara ta 2003 ministan yada labarai na kasar Iraki ya ki ya amince da gaskiyar cewar tuni tankokin yakin Amurka suka ja daga a sansanoni daban-daban a birnin Bagadaza, amma su kansu al’umar Irakin da ma mutane a sauran sassa na duniya baki daya sun ankara da cewar a daidai wannan ranar an shiga wani sabon yayi an kuma kawo karshen wancan zamanin. Sojojin Amurkan tare da wasu ‘yan kasar Iraki ‘yan kalilan ba su yi wata-wata ba wajen rushe mutun-mutunin Saddan Hussein, wanda aka rika nunarwa kai tsaye a gidajen telebijin na kasa da kasa. A wancan lokaci kuwa ba wanda ke da wata masaniya a game da alkiblar da kasar ta Iraki zata fuskanta daga bisani. Dukkan wadannan abubuwa sun faru ne shekaru hudu da suka wuce, amma har yau sai lalube ake cikin duhun a kokarin shawo kan rikicin kasar ta Iraki da ya ki ci ya ki cinyewa. An cafke Saddam Hussein aka zartar masa da hukuncin kisa bayan zaman sghari’arsa na tsawon watanni, amma duk da haka Iraki bata samu zaman lafiya ba, ballantana a yi batu game da kwanciyar hankali. A maimakon haka al’amura sai dada rincabewa suka yi, inda kasar ta tsunduma cikin wani mawuyacin hali mai kama da yakin basasa tsakanin al’umarta mabiya addinai dabam-dabam tare da samun taimako daga wasu kungiyoyi na ‘yan ta’adda da kuma wasu dauloli na ketare. Kasar ta Iraki na fuskantar mummunar barazana ta wargajewa duk da kokarin da ake yi na mayar da ita abin koyi a fannin mulkin demokradiyya a tsakanin kasashen yankin. An gudanar da zabe na demokradiyya aka yi ,kuri’ar raba gardama akan daftarin tsarin mulkinta, wanda ya zama kyakkyawan sharadin samun ci gaba a mulki na demokradiyya. Amma fa ga alamu zabe da daftarin tsarin mulki ba su ne kawai ake bukata ba. Kazalika akwa matsalar sojojin mamaye na Amurka, wanda har yau ba wanda ya san lokacin da zasu janye duk da kokarin da ake yi na ganin hakan ya faru, musamman daga bangaren jam#iyyar democrats ta Amurkan. Akwai ma masu hasashen cewar hatta wata gwamnati ta ‘yan demokrats da zata gaji kujera daga George Bush ba zata janye sojojin daga Iraki ba. A dai halin da ake ciki yanzun ba wanda ya san adadin sojojin Amurka da aka kashe a Iraki kuma kullun al’amuran tsaro sai dada tabarbarewa suke yi su kuma al’umar Iraki sune suka fi jin radadin matsalar. A takaice kifar da mulkin shugaba Saddam Hussein bai kawo wa al’umar iraki Sa’ida ba, a maimakon haka ya zama wani mataki ne na farko akan hanyar shiga wani hali mafi muni a cikin tarihin kasar.