Iraki: An kashe mutane 20 a kasuwa | Labarai | DW | 21.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki: An kashe mutane 20 a kasuwa

Mutane 20 sun mutu, a wani harin bam da dan kunar bakin wake ya kai a cikin babbar mota a kusa da kasuwar garin Tuz Khurmatu da ke kudancin birnin Kirkuk.

Jami'an 'yan sanda da likitoci a asibitocin da ke arewacin Iraki sun tabatar da jikkatar fararen 40, inda ake fargabar adadin mutuwar ka iya karuwa sakamakon mumunan raunuka da harin yahaddasa.

Ma'akatar cikin gida a kasar Irak, sun yi Allah wadai da wannan mumunar harin. Babu kungiyar da ta dau alhakin wannan harin, amma yankin ya sha fuskantar zafafan hare-haren kungiyar I S.Sojoji sun gama da kungiyar I S a Iraki

DW.COM