Ingila za ta yaki halasta kudadan haramu | Labarai | DW | 28.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ingila za ta yaki halasta kudadan haramu

Firaministan Britaniya David Cameron ya kudiri aniyar yaki da masu halasta kudadan haramun da kuma sauran masu satar kudade a kasashensu su na sayen kaddarori a Britaniya.

Cameron ya ce kasarsa bazata zama baboyar barayi ko ta masu halasta kudadan haramu ba. Ana sa ran Firaministan na Britaniya zai tabo wannan batu a wani jawabi da zai yi a wannan Talatar yayin wani rangadi da ya soma a Asiya ta Kudu maso Gabas, inda ake sa ran zai bayyana yuyuwar jin ra'ayin jama'a kan batun samun haske ga mallakar kaddarorin kanfanonin kasashen waje a kasar ta Britaniya ganin yadda halasta kudadan na haramu ke haddasa mugunyar tsadar gidaje a wannan kasar.

Cameron ya ce ya na son kasar ta Ingila ta kasance kasa da tafi ko wace kasa buda hannayanta domin karbar duk wasu masu zuba jari, amma kuma ta hanyar dukiya wadda ba ta haramun ba. A karo na farko dai a Kaka mai zuwa ma'aikatar haraji ta ingila, zata wallafa bayannai kan kaddarorin kanfanonin kasashen waje da ke wannan kasa.