1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Ingila ta kai wasan karshen na kasashen Turai

Suleiman Babayo USU
July 11, 2024

Ingila ta kai wasan karshe na neman cin kofin kasashen Turai da Jamus take daukan nauyi, bayan ta doke Netherlands biyu da daya, a wasan kusa da na karshe. Yanzu kasashen Ingila da Spaniya za su fafata wasan karshe.

https://p.dw.com/p/4i8uU
Kwallon kafa | Euro 2024 | Netherlands da Ingila
Wasan Ingila da Netherlands a gasar neman cin kofin kasashen TuraiHoto: Martin Meissner/AP/dpa/picture alliance

Ingila ta kai wasan karshe na neman cin kofin kasashen Turai. Ingila ta samu nasara kasar Netehrlands da ci 2 da 1, lokacin fafata a wasan jiya Laraba a birnin Dortmund na yammacin Jamus a wasan kusa da na karshe. Ita dai kasar da Jamus take daukan nauyi wannan gasa mai tasiri.

Karin Bayani: Aski ya zo gaban goshi a gasar Euro 2024

Ranar Lahadi mai zuwa ake kammala wasan inda za a tantance kasar da za ta lashe wannan kofi tsakanin Spaniya da Ingila. Ita dai Spaniya ta kai wasan karshen bayan doke Faransa da ci 2 da 1 a wasan kusa da na karshe. Kuma yanzu tsakanin Spaniya da Ingila za a tantance kasar da za ta lashe wannan kofi na Turai.

A can ma yankin Amirka, Ranar Litinin mai zuwa za a kara wasan karshen na cin kofin nahiyar na Copa tsakanin kasashen Ajentina da Kwalambiya. Ita dai Ajentian ta kai wasan karshen bayan Kanada 2 da nema a wasan kusa da na karshe, sannan ita kuwa Kwalambiya ta doke Uruguay da mai ban haushi.