Ingancin shinkafa da Alkama na fuskantar barazana a duniya | Labarai | DW | 02.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ingancin shinkafa da Alkama na fuskantar barazana a duniya

Sakamakon wani bincike ya nunar da cewa karuwar gurbatacciyar iska a sarari na barazana ga inganci wasu nau'o'in abincin na shinkafa da alkama da ga lafiyar dan Adam a kasashe masu tasowa nan zuwa shekara ta 2050. 

Sakamakon wani bincike da wata jaridar mai suna Health Perspective da ke wallafa labarai kan matsalolin muhalli ta fitar ya nunar da cewa karuwar gurbatacciyar iska a sararin samaniya na iya rage inganci wasu abincin cimaka kamar su shinkafa da alkama tare da haddasa matsaloli na kiwon lafiyar dan Adam a kasashe masu tasowa nan zuwa shekara ta 2050. 

Sakamakon binciken wanda gidauniyar Bill& Melinda Gates ta dauki nauyin gudanar da shi, ya nunar da cewa karuwar gurbatacciyar iska din a sarari na taimakawa ga tsunmburar da akasarin shukoki. 

Nau 'o'n cimakar na iya rasa sama da kashi 5% na sinadarensu masu tasiri a jikin dan Adam a cikin kasashe 18  na zuwa tsakiyar wannan karni a cewar binciken wanda wasu kwararru na sashen kiwon lafiya na jami'ar Harvard suka gudanar. Mutane kimanin miliyan 150 ne za su iya fuskantar barazanar karancin sinadaran abinci kamar su kalwar Proteine a cikin abin cin nasu.