INEC watakila ta dage zabe a Najeriya | Labarai | DW | 04.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

INEC watakila ta dage zabe a Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Tarayyar Najeriya INEC ta sanar da cewa akwai yiwuwar dage zaben kasar da za a gudanar a cikin wannan wata na Fabarairu da muke ciki.

default

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa daya daga cikin kwamishinonin hukumar zaben ta Najeriya Amina Zakari ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ta gudanar, inda ta ce in har ba a samu nasarar bayar da katunan zabe na din-din-din yadda ake bukata ba nan da ranar takwas ga wannan wata na Fabarairu kamar yadda hukumar ta tsara, to tabbas za a iya dage lokacin gudanar da zabukan na Najeriya, sai dai ta ce har kawo yanzu hukumar ba ta yanke hukunci kan matakin ba. Yazuwa yanzu dai wadanda suka can-canci kada kuri'ar a Najeriya miliyan 44 ne kadai suka karbi katunan zaben na din-din-din daga cikin sama da miliyan 68, a dai-dai lokacin da ya rage kwanaki 10 kacal a gudanar da zabukan na Najeriyar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal