1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane shida a rikicin siyasar Indonesiya

Abdourahamane Hassane
May 22, 2019

A Indonesiya mutane shida suka mutu kana wasu darurruwa suka jikata a taho mu gama da aka yi tsakanin jami'an tsaro da magoya baya 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/3Iuge
Indonesien Jakarta - Demonstrationen zum 1. Mai
Hoto: Reuters/W. Kurniawan

'Yan sandar sun tarwatsa masu yin gangamin da kulake da barkonon tsohuwa a jajibirin bayyana sakamakon zaben shugaban kasar wanda dan takarar adawarPrabowo Subianto a fadi a gaban shugaba Joko Widodo mai barin gado. 'Yan sandar sun ce sun cafke magoya bayan 'yan adawar kusan guda 70 wadanda ake zargi da tayar da fitina.