Indonesia ba ta ji dadin matakin da Denmark ta dauka ba | Labarai | DW | 12.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indonesia ba ta ji dadin matakin da Denmark ta dauka ba

Gwamnatin Indonesia ta soki matakin da Denmark ta dauka na janye jami´anta na diplomasiya da kuma ma´aikatan ofishin jakadancinta daga birnin Jakarta bayan zanga-zangar da musulmi suka yi don nuna fushinsu da zane-zanen batanci ga Annabi Mohammad SAW da wata jaridar Denmark din ta buga. Ma´aikatar harkokin wajen Denmark ta kuma gargadi ´yan kasar da su gaggauta ficewa daga Indonesia saboda dalilai na tsaro da kuma barazana da suke fuskanta a wannan kasa. Ministan harkokin wajen Indonesia Hassan Wirajuda ya bayyana wannan mataki da cewa riga malam masallaci ne kuma babu wani kwakkwaran dalili da zai sa Denmark ta janye jami´an diplomasiyarta. Kasar dai ta kuma janye jakadunta daga Syria da Iran. Har wayau dai ana ci-gaba da gudanar da zanga-zangar yin tir da cin mutuncin al´umar musulmin, inda a jiya aka gudanar da jerin zanga-zanga a biranen London, Paris da kuma Düsseldorf.