Indiya: Musulmi na fargaba kan rayuwarsu | Labarai | DW | 27.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indiya: Musulmi na fargaba kan rayuwarsu

Musulmi a India na fargabar rayuwarsu bayan barkewar rikicin kabilanci da na addini a birnin New Delhi

An tilasta wa iyalai da dama barin gidajensu bayan da rikicin da ya barke a tsakanin kungiyoyin 'yan Hindu da kuma Musulmi ya kara yin kamari a babban birnin kasar na India. Rahotanni sun ce an ga wasu gungun yan Hindu na afka wa unguwannin musulmi.

Tun farko a ranar Alhamis an tashi da zaman dar-dar a New Delhi, kwanaki biyu bayan tarzoma da kone-kone da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 30 da kuma jikkata wasu mutanen 250, abin da ke zama tarzoma mafi muni da ta afka wa birnin a tsawon shekaru da dama.

Zanga-zangar ta baya bayan nan ta samo asali ne kan bore game da wata doka mai sarkakiya da aka yi wa gyara ta zama dan kasa wanda musulmi a Indiya suka bayyana damuwar cewa za ta mayar da su saniyar ware.

Amirka ta bukaci Indiya ta martaba yancin yin gangami na lumana tare da yin kira ga dukkan bangarorin su kaucewa tashe-tashen hankula.