Indiya: Gurbatatar barasa ta kashe sama da mutane 100 | Labarai | DW | 11.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indiya: Gurbatatar barasa ta kashe sama da mutane 100

Mutane akalla 116 aka ba da rahoton cewar sun mutu a Jihar Uttar Pradesh da ke a arewacin Indiya, ya yin da wasu da dama suke kwance a asibiti suna yin jinya saboda amfani da gurbatatar barasa.

Yawancin wadanda suka mutu sun cikka ne a karshen mako bayan da suka sha barasar suka yi tilip. 'Yan sanda sun ce sun kama wasu wadanda ake zargi da laifin sarafa barasar har mutu kusan dubu uku.