1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro kan sauyin yanayi: Akwai alfanu?

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 27, 2019

Al'ummomin kasa da kasa da suka hadar da kawararru da kuma masu ruwa da atsaki kan al'amuran da suka shafi muhalli, kan yi tarurruka masu yawa a duk shekara da nufin lalubo hanyar magance matsalar sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/3LCTt
Afrikas Grüne Mauer im Sahel | Senegal, Akazien
Kwararowar hamada na da ga cikin manyan kalubalen sauyin yanayi a AfirkaHoto: Getty Images/AFP/S. Diallo

Matsalar sauyi ko dumamar yanayi, matasala ce da tuni ta zama ruwan dare gama duniya. Illolin sauyi ko dumamar yanayi sun hadar da kwararowar hamada da fari da ambaliyar ruwa da tsananin zafi da sanyi. Kwararru da masu ruwa da tsaki kan yi tarurruka domin lalubo hanyoyin da za a bi a shawo kan wannan matsala da ke kokarin zama ta gagari kundila.