Illolin ambaliyar ruwa a ƙasar Mozambik | Siyasa | DW | 29.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Illolin ambaliyar ruwa a ƙasar Mozambik

Dubunan al'umar Mozambik na cikin halin ƙaƙa ni ka yi dalili da mummumar ambaliyar ruwa.

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu yayin da wasu dubbai suka rasa muhallinsu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a kudancin ƙasar Mozambik.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa ambaliyar ruwan wadda ta kasance irin ta ta farko a tarihin ƙasar ta Mozambik, ta tilastawa kimanin mutane dubu 150 barin gidajensu yayin da kuma wasu 40 suka rasa rayukansu.

Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Patricia Nakell ta shaidawa manema labarai cewa, adadin na iya ƙaruwa sakamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske da ke yaɗa wannan ambaliyar ruwa zuwa arewaci.

A photograph made available 03 September 2009 shows residents of Ouagadougou attempt to navigate down a flooded road in Ouagadougou, Burkina Faso 01 September 2009. Annual torrential rain has caused flooding in almost all districts of the country. At least five people are reported dead and more than 150000 homeless following the heavy rains in Ouagadougou and its suburbs. EPA/PANAPRESS +++(c) dpa - Bildfunk+++

Tuni dai hukumomin ƙasar su ka fara ɗaukar matakai da suka haɗar da kafa sansani domin waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa.

Shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasar Mozambik Rita Ameida ta ce suna duba irin matakan da ya kamata su ɗauka domin taimakawa mutanen da wannan bala'i ya afkawa:Abun da mu ka tabatar da shi ya zuwa yanzu shine adadin farko na mutanen da abin ya shafa. Da gaske ne mun samu rahotanni da ke nuna cewa wasu mutanen sun ɓace, kuma mun haƙiƙance cewa wannan adadi na iya ƙaruwa a kwanaki masu zuwa. Muna aiki a wannan yanki, kuma ina ga a kwanaki masu zuwa zamu samu iya adadin waɗanda abin ya shafa.

A nasa ɓangaren Daraktan hukumar samar da ruwa ta ƙasar Rute Nhamugava ya ce, an fara samun raguwar wannan matsalar a kudancin ƙasar da abin yafi shafa.

Yace: A ɓangaren kudanci an samu raguwa kuma muna zubar da ruwa da yawa a hankali ya zuwa yanzu muna zubar da kimanin mita 50 na ruwa a sakan guda.

Ana dai tsammanin ɓallewar cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria a ƙasar ta Mozambik sakamakon wannan mummunar ambaliyar ruwa, hakan ce ma ta sanya Daraktan kiwon lafiya a babban birnin ƙasar wato Maputu P'ascoa Wate ya ce sun ɗauki ƙwararan matakai domin rage yaɗuwar wannan cuta.

Yace:Muna sane cewa sakamakon ruwan sama da akeyi yawan sauro zai karu, wanda kuma zai kara yawan masu kamuwa da cutar zazzabin Malaria. Wannan ne ya sa zamu yi kokarin kare sansanin da muka kafawa wadanda abin ya shafa daga sauro yayin ruwan sama.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Jaafar.
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin