1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar tashin hankali ga tattalin arzikin Masar

August 16, 2013

Rikicin siyasa tare da zubar da jini a Masar, yana haddasa mummunar illa ga tattalin arzikin kasar da ta dogara ga maziyarta daga ketare.

https://p.dw.com/p/19R3C
Hoto: picture-alliance/dpa

Yawan maziyarta dake shiga cikin kasar saboda yawon bude ido ya ragu matuka, kamar yadda kamfanonin Jamus masu shirya tafiye-tafiye da yawon shakatawa suka nunar. Haka nan kuma, kamfanonin ketare sun fara dakatar da aiyukan da rassansu suke yi a kasar ta Masar, ko da shike kungiyar yan kasuwa da msu masana'antun Jamus tace kamfanonin kasar dake Masar ba zasu janye gaba daya ba, saboda ya zuwa yanzu, babu wasu kwararan dalilai na daukar wannan mataki.

Kamfanoni da masana'antunmu dake can ba za su mika wuya tun a yanzu ba, inji jami'in kula da dangantakar tattalin arziki da ketare na cibiyar yan kasuwa da ma su masana'antun Jamus, Volker Treier. Yace kamfanoni da masana'antun na Jamus da yawansu ya kai 80 a Masar, suna daukar akalla Misirawa dubu 24 ne aiki. To sai dai wadannan kamfanoni ya zama ajibi yanzu su rufe ko su dakatar da wuraren aikin na su, saboda tashin hankalin ya jawo katsewar hanyoyin samun kayaiyakin sarrafawa a cikinsu.

Kamfanin da shine na biyu wajen girma a duniya dake kera kayaiyakin amfanin gida, wato Electriolux ya dakatar da aiyukansa a Masar har sai abin da hali yayi, abin da ya shafi ma'aikata akalla dari bakwai, ko da shike wani kakakin kamfanin yace ranar Asabar za'a yi nazari, a sake duba yiwuwar sake bude masa'naantar. Kazalika, kamfanin General Motors dake kera motocin Opel, yace ya dakatar da aiyukansa a reshen masana'antar dake kusa da birnin Alkahira, matakin da ya rutsa da ma'aikata akalla 1400.

Ägypten Hurghada am Roten Meer
Jiragen ruwan masu yawon bude ido kan kogin NilHoto: picture-alliance/dpa

Kamfanin man fetur mafi girma a duniya, wato Shell shima ya rufe ofisoshinsa a kasar. Damuwar da ake nunawa game da ko tashin hankalin na Masar zai iya kawo cikas ga suhurin danyen man fetur dake wucewa ta mashigin Suez, ya sanya farashin man yayi tashin gwauron zabo a kasuwannin duniya, inda farashin ganga guda ta dnyen mai ya kai akalla dollar 111, farashi mafi tsanani cikin watanni hudu.

Ga batun yawon bude ido a Masar kuwa, tashin hankalin da kasar ta fada a baya-bayan nan ya zama mummunan abu. Kasar mai yawan jama'a miliyan 84, ta dogara ne matuka ga kudin da take samu daga ziyarce-ziyarce da yawon bude ido daga ketare. Adadin masu neman kai ziyarar bude ido a kasar yanzu, ko kadan bai kusanci adadin da aka samu misalin Euro miliyan dubu 10 a zamanin juyin juya hali na farko a kasar ba, saboda tun bayan wannan lokci yawon bude ido a Masar din ya ragu ya ragu da misali kashi daya cikin kashi ukku, yayin da a sakamakon tashin hankalin na baya-bayan nan tafiye-tafiyen bude ido misali ta jiragen ruwa kan kogin Nil ko wuraren tarihi suka gagara.

Kamfanonin yawon bude ido na Jamus a madadin haka, sukan baiwa masu hulda dasu tayin kai ziyarar shakatawa a wuraren dake nesa da inda tashin hankalin yake, misali a kusa da tekun Bahar-Maliya. Sybille Zeuch, kakakin kungiyar kamfanonin yawon shakatawa na Jamus, tyayi byanin cewa:

Tourismus in Ägypten
Koma bayan masu yawon shakatawa a MasarHoto: picture-alliance/dpa

"Masu hulda damu suna da yancin canza tsarin hutunsu, kuma wajibi neda mai tafiyar da masu shirya tafiyar su daidaita da juna, ko da shike ya zuwa yanzu, ba'a sami masu soke shirinsu na yawon shakatawa a Masar ko masu canza tsarin hutun nasu da yawa ba. Haka nan bamu da wani labari na karin masu bukatar yanke hutunsu a Masar su komo gida ba."

A halin da ake ciki, ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta kara tsananta gargadinta a game da yadda tsaro yake a Masar. M'aikatar harkokin wajen a Brlin tace akwai tsoron cewar halin tsaro zai kara tabrbarewa a birnin Alkahira, yayin da ake sa ran za'a sami zanga-zanga a duk fadin kasar.

Mawallafi: Wenkel/Umaru Aliyu
Edita: Saleh Umar Saleh