1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar kaciya wa yara mata

September 19, 2013

A ko wasu dakiko 11, ana yi wa kananan yara mata kaciya, ta hanyar yanke matuncinsu da wuka ko reza ko kuma almakashi.

https://p.dw.com/p/19k0b
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan dabi'a dai tafi yaduwa a nahiyarmu ta Afirka sai kuma yankin Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya ke mara musu baya. To a kan wannan lamarine aka bude wata cibiya a Berlin babban birnin kasar Jamus, ta kwararrun likitoci dake yiwa wadanda aka yiwa kaciyar tiyata domin gyara raunin da aka ji musu sakamakon kaciyar.

Ita dai wannan cibiya da ta kasance irinta ta farko an bude ta ne da taimakon wata gidauniya mai suna “Desert Flower Foundation” da wata mai faftuka 'yar kasar Somaliya Waris Dirie take gudanarwa.

Yi wa mata kaciya da akafi sani da suna a aturance da "Female Genital Mutilation" ana yiwa yara mata da shekarunsu bai wuce hudu a duniya ba, wanda kuma ke haifar musu da matsaloli da cututtuka har zuwa girmansu, musamman idan suka yi aure yayin saduwa da mazajensu da kuma sanda suka zo haihuwa.

Wata 'yar asalin kasar Habasha Senait Demisse, da ke da kimanin shekaru 34 a duniya, wadda a yanzu haka take shirin zama mace ta farko da likitocin wanannan cibiya za su yi wa aiki na daya daga cikin matan da aka yiwa kaciya suna kanana, ta bayyana cewa tana iya tuna sanda aka yi mata kaciyar ita da wasu kawayenta biyu.

Ta ce "Ina 'yar karamata sai dai ba zan iya tuna shekaru na ba ina ga ina shekaru shida ko bakwai, na yi kokarin in gudu amma sai da suka kamoni, daga nan ba zan iya tuna abin da ya faru da ni ba ina ga na suma ne ban san abin da ya faru bayan nan ba".


Demisse, wadda a yanzu haka take zaune a kasar Poland, ta ce ta samu labarin wannan cibiya ta "Desert Flower” inda nan take ta daura aniyar zuwa domin tace tana so ta zamo cikakkiyar mutum a yanzu ta kuma ce bata fargabar shiga dakin tiyata.

Likitoci da dama ne dai suke gudanar da aikin tiyatar ga matan da aka yiwa kaciyar, sai dai a cewar daya daga cikin likitocin Dr. Roland Scherer, da yake jagorantar sabuwar cibiyar da gidauniyar "Desert Flower" ke daukar nauyi ya ce aikin da akwai wahala:

Ya ce "Ba tiyata ce mai sauki ba, saboda an riga an yi musu rauni shekaru da dama da suka wuce, sabo da haka akwai ciwuka da yawa a gurin, gaskiya ana bukatar kwararru da dama kafin gudanar da tiyatar".

A wannan sabuwar cibiya daya daga cikin matan da aka yiwa kaciya 'yar asalin kasar Somaliya Waris Dirie ke jagoranta, ana bawa matan shawarwarin yadda za su kula da kansu kyauta tare da wayar musu da kai.

Waris Dirie ta ce ta kirkiro wannan cibiya ne domin yaki da wannan mummunar al'ada dake jefa mata cikin wahala.

Berlin Eröffnung Desert-Flower-Center Krankenhaus Waldfriede
Hoto: imago/epd

Ta ce "Ba shi da wani amfani, wannan ta'addanci ne tsantsa da cin zarafi da kuma rashin adalci ga kananan yara".

Ita kuwa Senait Demisse, cewa ta yi ta dauki aniyar komawa kasarta domin wayar musu da kai musamman ma kananan yara, ta hanyar koyar da su kiran 'yan sanda in za a yi musu kaciya domin su fara yakar abin da kansu.

Mawallafiya: Lateefah Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu