1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Igiyar ruwa ta koro gawarwakin 'yan cirani

Ramatu Garba Baba
December 27, 2021

Igiyar ruwa ta kora gawarwakin 'yan cirani 28 gabar tekun ruwan Libiya, bayan nutsewar kwale-kwalensu a yayin da suka yi kokarin bin barauniyar hanya don shiga nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/44s4R
Europa | Seenotrettung im Mittelmeer
Hoto: Renata Brito/AP Photo/picture alliance

Rahotanni daga kasar ta Libiya sun nunar da yadda igiyar ruwa ta koro gawarwakin 'yan cirani 28 gabar tekun kasar, bayan nutsewar kwale-kwalensu a yayin da suka yi kokarin bin barauniyar hanya don shiga nahiyar Turai a karshen makon da ya gabata. Rahotan ya kara da cewa, an dauki kwanaki da samun nutsewar kwale-kwalen gabanin samun gawarwakin a gabar ruwan mai tazarar kilomita casa'in daga birnin Tripoli. 

Mashigin ruwan Libiya a baya-bayan nan, ya kasance a matsayin babbar hanyar da ‘yan cirani ke amfani da ita don tsallakawa Turai duk da yadda suke rasa rayukansu a kowacce rana. Wannan Ibtila’in na zuwa ne kwanaki kalilan bayan mutuwar ‘yan cirani 160 a dai hanyar ta Libiya cikin kasa da mako guda wanda ya mayar da adadin rayukan da aka rasa cikin shekarar nan zuwa mutum dubudaya da dari biyar.