ICC za ta gudanar da bincike a Falasdinu | Labarai | DW | 16.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ICC za ta gudanar da bincike a Falasdinu

Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta ce ta bude babin farko na bincike kan aikata laifukan yaki a Falasdinu.

Wannan dai shi ne matakin farko a hukumance da aka dauka wanda ka iya kaiwa ga tuhumar Isra'ila kan aikata laifukan yaki a Falasdinun. Babbar mai gabatar da kara a kotun ta ICC Fatou Bensouda ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike a matakin farko mai cikakken 'yanci wanda ba nuna banbanci a ciki. A ranar daya ga wannan wata na Janairu da muke ciki ne dai mahukuntan Falasdinun suka bukaci kotun da ta gudanar da bincike kan abubuwan da Isra'ila ta aikata a yankin Zirin Gaza tun daga watan Yunin shekarar da ta gabata ta 2014, kafin washe gari su mika bukatarsu na zamowa mamba a kotun ta ICC.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal