ICC ta yi watsi da buƙatar sakin Gbagbo | Labarai | DW | 27.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ICC ta yi watsi da buƙatar sakin Gbagbo

Babbar kotun duniya da ke hukunta manyan laifukan yaƙi ta yi watsi da buƙatar da lauyoyin tsohon shugaban ƙasar Côte d'Ivoire suka gabatar na a yi masa sakin wucin gadi.

Lauyoyin Gbagbo suka ce sakin wucin gadi zai ba wa tsohon shugaban Côte d'Ivoire samun ƙarin kuzari da lafiya wajen fuskantar shari'a da za a yi masa nan gaba. A lokacin da ya ke magana a wani zaman da kotun ta yi babban alƙali mai gabatar da ƙara ya sanar da cewar ba da belin Laurent Gbagbo mai yawan magoya baya na iya zama barazana ga ci gaba da gudanar da bincike a shari'ar da za a yi masa.

Tsohon shugaban mai shekaru 67 da haifuwa wanda ake tsare da shi a kotun ta duniya da ke a birnin Haye tun a cikin watan Mayon shekara ta 2011, ana tuhumar sa da aikata kisan gila akan farar hula a lokacin da aka gudanar da zaɓɓukan ƙasar a shekarun 2010 zuwa 2011.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohamadou Balarabe Awal